– A jya ne shugaban kasa ya tattauana da manyan jam’iyyar APC
– Mataimakin shugaban kasa, shugaban jam’iyya, Atiku, Tinubu duk sun halarta
– Bukola Saraki bai samu halarta ba
A jiya ne shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya tattauna da shugabanni APC a fadar shugaban kasa.
KU KARANTA: Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata
Manya manyan jam’iyyar duka sun halarta sai dai shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne kawai ba’a gani ba.
Mataimakin shugaban kasa, kakakin majalisar wakilai, shugaban jam’iyya, Tinubu, gwamnoni da yawa duka sun halarata.
Jaridar The Punch ta bayyana cewa toshon mataimakin shugaban kasa Atiku ya halarci taron, amma yazo ne kimanin mintuna 20 bayan da taron ya fara.
Ga wasu hotuna nan,
Shugaba kasa, shugaban jam’iyar Apc tare da kakakin majalisar wakilai
Shugaba Buhari tare da Bola Ahmad Tinubu
Gwamnonin Jigawa, Ogun da Bauchi a taron na APC
Wasu Ministocin a wurin taron
Jerin shugabannin jam’iyyar akan babban tebur
Wannan taron na zuwa ne kwanaki kadan bayan da akayi zaben cika gurbi na jihar Rivers, shari’ar Bukola Saraki da kuma Allah wadai da gwamna Fayose yayi ma Buhari.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin samada sa wutar lantarki tsayayyiya a Najeriya. Shugaban kasan ya bayyana wannan ne a taron zauren tattalin arziki na kasa wanda ya bude da kanshi a wannan shekarar a babban birnin tarayya, Abuja.
The post Buhari ya tattauna da shugabannin jam’iyyar APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM http://ift.tt/25lpHgb
via IFTTT
Post a Comment