– Hukumar DSS ta saki Afolabi Akande
– An kwantar da shi a wani asibiti a Abuja
– Ana duba lafiyar sa
Dan majalisar Ekiti, Afolabi Akande a asibit bayan da hukumar DSS ta sake shi
Hukumar DSS ta saki dan majalisar jihar Ekiti, Afolabi Akande, wanda ta tsare. Bayan da DSS ta sake shi, ba’ayi wata wata ba sai aka garzaya dashi asibiti domin jikin shi yayi rauni sosai.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tattauna da shugabannin jam’iyyar APC
Dan majalisar ya kwashe kwanaki 18 a hannun DSS kafin su sake shi a jiya. Ya sha fada masu cewa shi ba shi da lafiya kain su kama shi.
Afolabi ya bayyana ma yan jarida cewa DSS sun bashi maganin zazzabin sau 2 domin sau 2 yana faduwa saboda zazzabinncizon sauro.
Afolabi ya bayyana cewa jami’an hukumar DSS basu gaya mashi dalilin daya sanya suka kama shi ba. Amma ya zargi cewa sun sake shi ne saboda tsanantar rashin lafiya da yake ta fama da ita.
Afolabi a kwance a asibiti bayan da DSS ta sake shi
Shugaban kwamitin labarai na majalisar Jihar Ekiti, Gboyega Aribisogan, ya bayyana cewa duka mutanen jihar ta Ekiti sunyi murna sosai da aka sakar masu dan majalisar su na jihar Ekiti.
” Duka muna murna da sakin Afolabi Akande.
“Gwamna Ayodele Fayose ya bada umurni a kai shi asibiti domin kula da lafiyar shi.’
Idan za’a iya tunaw, jami’an DSS sun shiga majalisar jihar Ekiti a ranar 4 ga watan Maris inda suka tafi da Afolabi Akande.
Daga baya sai suka tafi dashi Abuja inda suka cigaba da tsare shi duk da cewa babbar kotun tarayya dake Ado Ekiti ta bada umurni a sake shi a kuma bayyanar dashi a ranar 16 ga watan Maris. Hukumar DSS dai taki yin biyayya ga kotun.
The post Hukumar DSS ta saki dan majalisar Ekiti data tsare appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM http://ift.tt/1WHq66J
via IFTTT
Post a Comment